Amarya ta cinye kazar amarci kafin Ango ya gama sallar nafila

Rabin rayuwar namiji sana’a mai kyau, don samun rayuwar auren farin ciki dole sai kana da sana’a mai kyua.

Rayuwata miƙaƙƙen layi ce, daga gida sai wajen aiki, domin cimma Can-can-ce Can-can-ce na rayuwa to kana buƙatar jajircewa da maida hankali. Kamar dai yanda muka saba yauma nazo maku da wani ƙayateccen labari, wanda zai saku nishaɗi.

Wata Amarya ta cinye kazar Amarci kafin ango ya gama sallar nafila.

Kamar dai yanda kuka sani al’adar mu ta hausawa idan namiji yayi sabon aure to abokai sayi kayan lallashin Amarya irin su; gasashshiyar kaza, Lemun roba da sauran kayan makulashe domin su raka shi ɗakin Amarya.

To haka shima wannan angon ta faru dashi, bayan abokai sun tafi sai ango yayi alwala domin gabatar da sallar nafila yayin da ya bar Amarya cikin ɗaki.

Bayan ya idar da Sallah ya dawo domin su fara cin abinda abokai suka kawo masu, bisa mamaki sai ango yaga amarya har ta cinye kaza.

Shin a ganin ku menene ya kawo hakan??

source by Hilal Haruna

Views: 51

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *