Amurka ta ce bata yarda Najeriya ta yaƙi ƴan bindigar daji da jiragen da ta siyar mata ba

Ba mu yarda a yaki ‘yan fashin daji da sabbin jiragen yaki na Super Tucano A-29 da Gwamnatin Najeriya ta sayo ba, don ba ‘yan ta’adda bane in ji Amurka kamar yadda shafin Sokoto Online ya ruwaito.

Tun bayan isowar jiragen Najeriya a watan Yuli bayan kammala ciniki, ƴan ƙasar da dama sun saka ran cewa nan da nan za a fara amfani da su wajen kai wa ƴan fashin daji hare-hare don murƙushe su, musamman a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Sai dai rahotanni sun ce akwai wani babban lamari da ke jawo tsaiko wajen aiwatar da hakan, wanda bai wuce sharaɗin da ke dabaibaye da sayen jiragen ba tun farko, wanda Amurka ta sanya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta shaida wa Majalisar Dokokin ƙasar cewa, tun farko Amurka ta yarda ta sayar da jiragen yaƙi na A-29 Super Tucano 12 ne idan za a yi amfani da su a kan ƴan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya ne kawai, ban da ƴan fashin daji.

Kenan batun a yi amfani da jiragen wajen yaƙi da ƴan fashin dajin da ke addabar yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya bai taso ba, tun da har yanzu gwamnatin Najeriya da gwamnatocin ƙasashen waje ba su ayyana su a matsayin ƴan ta’adda ba.

Ana ta ƙara samun kiraye-kirayen a ɗauki wannan mataki, don babu dama ga dakarun tsaron ƙasar su kai ƙarin kayan yaƙi da nufin murƙushe ‘yan fashin daji da suka addabi yankunan arewa maso yamma da sassan arewa ta tsakiya.

Amma Majalisar Wakilan Najeriyar ta bayyana fatan cewa nan ba da daɗewa ba, Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu kan ƙudurin da ke neman ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *