An ba shi gyaran Mota ya je daukar Budurwarsa da ita, Bishiya ta fado mata tayi kwandam

Rahotanni daga jihar Kadunan Najeriya, na cewa, wani bakanike ya je daukar Budurwarsa ya aje motar da aka ba shi gayara a kar kashin wata Bishiya, iska mai karfi ya turo Bishiyar kan motar ta yi kwandam baki dayanta.

A wani rahoto da jaridar Dimokuradiyya ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna photon motar ta lalace rahoton ya ce “An bashi gyaran mota, bayan ya gama gyara sai ya je daukar budurwarsa zuwa yawo, iskar ruwa kuma ta ture wannan bishiyar a kan motar”.

Kamar yadda jaridar ta Dimokuradiyya ta bayyana, irin wannan abu dai yana faruwa a cikin al’ummar mu ta yadda za’a bawa mutum gyaran abun hawa mota ko mashin amma ya hau ya je yana yawo da shi wajen abokai ko yan’mata wasu ma har cewa suke nasu ne, matsalar ta fi kamari tsakanin kanikawa da kuma masu sana’ar wankin ababan hawa.

Kunji fa shin idan taka ce zaka hakura ko kuwa sai ya biiyaka?

Views: 27

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *