Ku kalli yadda yan IPOB ke jifar yan arewa kamar shaidanu a Kudu

Wani fai fan bidiyo mai kimanin tsayin minti biyu ya nuna yadda wasu gun gun matasa da ake kyautata zaton yan kungiyar tada kayar baya ta IPOB suna jifar manyan mitocin daukar kaya, wato tirela, masu kai kayan masarufi daga arewa zuwa kudu.

A watannin da suka gabata dai yan arewa sun kwashi su a hannu sakamakon irin jerin hare haren da yan kudun ke kai musu, a wannan satin dai kungiyar arewa ta gar gadi al’ummar arewa da su kauracewa zuwa yankin kudancin Najeriya, domin tsira da dukiyoyi da rayukansu.

Kungiyar ta ce “Muna gargadin yan’arewa da su guji zuwa yankin kudanci har abubuwa su lafa” sai dai wasu sunyi burus da wannan shawara da kungiyar dattawan arewan.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *