Shahararren daraktan shirya fina finai a masana’antar Kannywood Malam Aminu Saira ya saki wani bangare daga cikin shahararren shirin nan nasa mai farin jini wanda aka fi sani da Labarina zango na ukku wato session 3 a shafinsa na sadarwa Facebook.
Shirin dai ya dade yana dauka tare da jan hankulan masu kallo a sassa daban daban na ciki da ma wajen Najeriya, kuma jama’a musamman masoya shirin sun zuba ido domin ganin sabon shirin ya sona fitowa domin su bawa idanuwansu abinci.
Yau dai jarumi Malam Aminu Saira, ya fitar da wani bangare daga cikin shirin wanda bai kai tsawon minti guda ba inda ya ce a gobe Juma’a za’a saki cikakkar tallar shirin dauke da ranar da za’a soma haska shi ga masu kallo da kuwa gurin da za’a haska shin.
Views: 37
