Da ɗumi-ɗumi: An Daina Amfani Da Tsoffin Koɗin ₦200, ₦500 da ₦1000 tun 10 ga wata —CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa tsohon takardun Naira na N200, N500 da N1000 sun zama mara amfani a Najeriya tun ranar 10 ga Fabrairu, 2023.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Konturola na Babban Bankin Najeriya (CBN), a jihar Bauchi, Haladu Idris Andaza a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin a babban bankin Najeriya CBN, reshen Bauchi.
Ya ce, “A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, tambayoyi daga bangarori daban-daban na jama’a sun cika mu, game da ka’idojin gudanar da ayyukanmu na tsofaffin takardun kudi, ta yadda za a yi, akwai tambayoyi da yawa a nan da can wadanda mutane ke da su.”
A cewarsa, “Don haka don kauce wa shakku, muna so mu bayyana cewa CBN a shirye yake kuma an bude shi don karbar duka waɗancan tsofaffin takardun kuɗi bisa wasu sharuɗa da aka gindaya.”
“Abokan ciniki suna da ’yanci su zo Banki su ajiye abin da ba za su iya ajiyewa a Bankunan Kasuwanci ba saboda an kama kuɗin a matsayin waɗanda suka daina amfani tun ranar 10 ga wannan watan Fabrairu na wannan shekarar 2023.
Source:by newsligth
From Opera News.
Views: 13
