“An kama ƴansanda 9 da ake zargin da hannunsu a garkuwa da ɗalibai 43 a Mexico

An kama ƴansanda 9 da ake zargin da hannunsu a garkuwa da ɗalibai 43 a Mexico

An kama jami’an ƴansanda tara a kasar Mexico dangane da bacewar dalibai 43 na kwalejin koyarwa ta Ayotzinapa Rural Teachers’ College a shekarar 2014.

Sakataren Tsaron Jama’a ta Jihar Guerrero me ya sanar da kamun a yau Alhamis.

Hukumar binciken manyan laifuka ta ce ta aiwatar da umarnin cafke jami’an ‘yansandan jihar bakwai da wasu mutane biyu a karamar hukumar Iguala.

A watan Satumbar 2014, dalibai 43 na kwalejin da ta yi suna wajen tsatstsauran ra’ayin kawo sauyi, su ka bace bayan da ‘yan lsanda suka kama su a hanyarsu ta komawa gida daga Iguala.

Daliban sun yi zanga-zangar nuna rashin goyon-baya ga bambancin da ake nunawa wajen ɗaukar malamai aiki.

An bayyana cewa, ‘yan sandan yankin sun tare hanyar da daliban ke tafiya, inda suka yi garkuwa da su tare da mika su ga ƴam fashin jeji da suka kashe daliban a wurare daban-daban.

Binciken gawarwakin kasusuwan da aka gano a yayin gudanar da bincike ya tabbatar da gano dalibai uku da ga cikin wadanda suka bata.

Har ila yau, shaidun abubuwan da suka faru, da masu hannu a ciki da kuma manyan shaidu 26, ya zuwa yanzu sun mutu ko kuma an kashe su yayin binciken.

source daily nigeria hausa

Views: 4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *