An Kama Ɗan sandan da ya ba Fasto Bindigar AK,47.
A yayin da rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ke binciken limamin cocin House on the Rock Church da ke Abuja, wanda ya hau kan mimbari da bindiga kirar Ak 47 a ranar Lahadin da ta gabata, wani sifeton ‘yan sandan da ke bakin aiki shi ma yana fuskantar hukuncin ladabtarwa.
An kama Fasto Uche Aigbe ne da sanyin safiyar ranar Litinin tare da babban jami’in tsaro na Cocin da wani Sufeto.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Josephine Adeh, Sufeto Musa Audu, wanda ke bakin aiki, ya bada bindigar sa ga Fasto ba tare da izini ko neman izinin hukumar ‘yan sanda ba.
A halin da ake ciki, ‘yan sanda sun bukaci jama’a da su yi watsi da ayyuka ko maganganun da suka saba wa wasu dokoki saboda za a hukunta duk masu karya doka.
By criminalfightersng
Views: 12
