An kashe wani mutum bayan samunsa da laifin ƙone Alƙu’ani mai girma a Pakistan

Shafin Labarun Hausa ya ruwaito cewa.

Wani mutumi da ake zargin sa da kone Alkur’ani Mai Girma a kasar Pakistan ya sheka barzahu sakamakon dukan da ya sha a hannun wasu fusatattun mutane dake garin Khanewal cikin lardin Punjab.

Ya zuwa yanzu dai wakilin Fira-Ministan kasar kan harkokin addini, Tahir Ashrafi, ya bada sanarwar kama mutane da dama.

Bisa zargin su da ake yi da kisan wannan mutumi, inda rahotanni suka bayyana cewa lamarin ya faru a ranar Asabar.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata biyu da suka gabata, inda a kasar ta Pakistan aka yiwa wani manajan masana’anta wanda ya fito daga kasar Sri Lanka dukan tsiya da har yayi sanadiyyar rayuwarsa, sakamakon kama shi da laifin batanci da aka yi.

Kamar yadda wani jami’in dan sanda ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, mutanen sun hadu a wani Masallaci ne a ranar Asabar da cikin dare, sai wani dan limami ya sanarwa da su cewa yaga lokacin da mutumin da ake zargin ya dauki shafukan Alkur’anin yake konawa.

Views: 35

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *