
Idan baku manta ba a farkon makonnan ne takaddama ta barke kan zargin da ake yiiwa Ummi Rahab inda har wasu ke cewa bata da asali dalilin da yasa aka bayyana hoton mahaifiyar ta daa kuma mahaifinnta wanda balarabe ne dake a kasar Saudiyya.
Shafin labarun Hausa ya bada rahoton cewa a wani sabon koke da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam, Muhammad Lawan Gusau ya kai ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, kan wani hoton takardar koken da Ummi Rahab ta kai ga hukumar ‘yan sandan farin kaya na CID, wacce ke zargin cewa Adam A Zango na bata mata suna.
Muhammad Lawan ya yiwa kwamishinan ‘yan sandan fashin baki kan koken da Ummi ta kai, kana ya nemi a mayar da ita kasarta ta haihuwa kamar yadda Yasir ya bayyana cewa ‘yar Najeriya ba ce.
Wannan koke nasa, bayan ya aikawa kwamishinan ‘yan sanda na Kadduna, ya kuma aika wani kwafin ga mataimakin kwamishina na CID, biyo bayan sakon da ke yawo da kuma maganganun da dan uwanta Yasir ya yi, ga dai yadda koken ya ke.
Takardar koken mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Agustan shekarar 2021, an aikata ne ga babban kwamishinan ‘yan sanda na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya fara da cewa:
Views: 75
