Umma Shehu ta bayyana sunayen yan Hisbar dake neman mata

A farkon makonnan ne hukumar Hisbah ta kama Sadiya Haruna Kabala wacce tayi kaurin suna wajenyada kalaman batsa a shafukan sada zumunta na zamani wato social media.

Sai dai biyo kama ta da akayi abokiyar aikinta Umma Shehu ta bayyana bacin ranta game da lamarin inda ta ce akwai masu neman mata a cikin yan Hisbar ma kuma zata bayya sunansu.

Biyo bayan kama Sadiya Haruna da hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi bisa zargin ta da yada bidiyon batsa da kuma kalamai na batsa da sunan tallan magani.

Jaruma Umma Shehu ta fito ta kalubalanci hukumar ta Hisbah, inda ta bayyana hakan shiga tsakanin Allah da bawan sa ne a karshe ta kare da cewa su kansu ‘yan Hisban akwai mazinata a cikin su, idan aka kureta za ta kama suna.

Sai da wannan kalamai na ta sun bata ran al’umma musammam masu kishin addini inda suke ganin a cikin maganganunta akwai karancin fahimtar addini, inda aka dinga yi mata raddi kala-kala wasu a rubuce wasu kuma suna mata bidiyo wanda hakan ya sa ta goge bidiyon daga shafinta.

Sai dai a safiyar yau muka tashi da labarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa hukumar Hisbah ta kama Umma Shehu ita ma a jihar Kaduna.

Views: 40

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *