
Fauziyta D Sulaiman ta wallafa hoton bidiyon wata baiwar Allah da kungiyar kiristoci suke yi mata tayin, ta var addinin Musulunci ta dawo kiristiyanity domin suyi mata maganin lalurar da take fama ta ita,
Bidiyon matar ya dauki hankali bayan an wallafa shi a shafin wata baiwar Allah mai taimakawa da zamewa mabukata tsani wajen nemo musu taimako a wurin al’umma ta hanyar yadawa a shafinta, musamman ma masu larura da aka rasa kudin magani ko masu daukar nauyi.
Gidauniyar Fauziyya Danladi Sulaiman, mai suna Creative Helping Needy Foundation ta shafe shekaru masu yawa tana aikin taimako irin wannan.
A shekaran jiya ne dai Fauziyya ta wallafa bidiyon baiwar Allah da ‘ya’yanta wacce ke fama da larura mai ban tausayi ta ciwon daji a mahaifa, wacce ta kai ga har sai da aka cire mata mahaifa, amma saboda rashin magani ya sanya aikin ya lalace, har ta kai ga gabanta yana fitar da tsutsotsi. ku kalli bidiyon don karin bayani ta wannan link.
https://www.instagram.com/tv/CTM23KqI3dC/?utm_source=ig_web_copy_link
KARIN LABARAI:
Views: 11
