
A ranar Alhamis ne Kwamitin da IG ya kafa domin gudanar da bincike game da badakalar Abba Kyari ya bada rahoton sa na karshe, inda wasu rahotanni ke cewa ma an wanke wanda ake zargi.
Sai dai tuni wasu daga cikin magoya bayan Abba Kyari irin su Datti suka bayyana ra’ayiyinsu game da batun ga abinda yake cewa.
ALBISHIR ZUWA GAREKU MASOYAN SARKIN YAKI
Yau Alhamis 26-8-2021 kwamitin binciken Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari karkashin jagorancin DIG Egbunike ya kammala binciken sa ya mika rahoton binciken wa Maigirma shugaban ‘yan sandan Kasarmu Nigeria IGP Usman Baba Alkali
Maigirma shugaban ‘yan sanda yana rike da rahoton binciken, idan ya kammala nazari akan sakamakon binciken zai mika zuwa ga masu iko da Gwamnatin Nigeria kafin a sanar da al’umma, kamar yadda sanarwa ya fito daga kakakin ‘yan sanda na kasa
Insha Allahu makiyan Sarkin Yaki zasuyi kukan bakin ciki, mahassada da munafukai da maciya amanar tsaron Nigeria zasu hadu da bugun zuciya saboda fargaba, yayin da masoya zasuyi murna da sujudush-shukr wa Allah Madaukakin Sarki
Ba zamuyi riga Malam Masallaci ba, amma ina wannan maganar ne da hujja da kwarin zuciya Wallahi
Jinjina gareka Sarkin Yaki dodon azzalumai maciya amanar tsaron Nigeria, wannan sharrin da suka maka babu abinda zai kara maka face daukaka, sunnar rayuwace ta ‘yan gwagwarmaya, akwai daukakar da bata zuwa sai da sanadi na sharri irin wannan
Yaa Allah Ka tsare mana rayuwar Sarkin Yaki DCP Abba Kyari, Allah Ka daukaka darajarshi zuwa matakin IGP Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
Views: 28

wow