Ana dab da rantsuwa an bankaɗo wani laifin Tinubu da ka iya hana a rantsar da shi

An nemi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya fayyace gaskiya kan wani fasfo da ke yawo wanda ya nuna shi a matsayin ɗan ƙasar Guinea Conakry.

Wata ƙungiyar magoya baya ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, mai suna Peter Obi Support Network (POSN), itace ta yi wannan kiran.

Obi yayi watsi da sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa inda yayi zargin cewa an masa maguɗi sannan zai tabbatar a kotu cewa shi ya lashe zaɓen.

Awka, Anambra – Ƙungiyar Peter Obi Support Network (POSN), ta buƙaci ɗan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da ya fayyace gaskiya kan zargin cewa shi ɗan ƙasa biyu ne.

New Telegraph tace ƙungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 17 ga watan Afirilu, inda ta ƙara da cewa dole ne Tinubu ya wanke kan sa kan batun da yake yawo a soshiyal midiya ana zargin sa da ɓoye cewa yana da ikon zama ɗan ƙasa a ƙasar Guinea.

Wakilin Legit.ng a Anambra, Mokwugwo Solomon, ya hakaito cewa wani hoton fasfo na ƙasar Guinea, mallakin Bola Tinubu, ya karaɗe shafukan yanar gizo bayan wani ɗan jaridan yanar gizo, David Hundeyin, ya sanya shi a Twitter.

A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar ya rattaɓawa hannu, Onwuasoanya Jones, yayi nuni da cewa shugabancin Tinubu na fuskantar babban haɗari saboda dokokin ƙasar nan sun samar da matsaya akan zama ɗan ƙasa biyu.

“Hankalin mu ya kai kan wani fasfon ƙasar Guinea Conakry na Bola Tinubu, wanda ya yaɗu a yanar gizo bayan ɗan jarida, David Hundeyin, ya sanya kwafin sa a shafin sa na Twitter.”

“Kowa yana sane da irin kyakkyawar alaƙar da ke a tsakanin shubagan ƙasar Guinea, Alhpa Conde, da Tinubu, inda har Tinubu ya taɓa bayyana cewa ya taimakawa Conde yin tazarce a Oktoban 2015.”
Ƙungiyar POSN ta ci gaba da cewa:

“Zargin zama ɗan ƙasa biyu da ake yiwa Tinubu ya sanya akwai buƙatar a binciki tsohon gwamnan jihar Legas kan zargin yin rantsuwa bisa ƙarya.”

“Tinubu bai bayyana komai ba dangane da zaman sa ɗan ƙasar Guinea a takardun da ya miƙa wa INEC domin zaɓen shugaban ƙasan Najeriya.”

“Da zargin zama ɗan ƙasa biyu da ake yi wa Tinubu, yana da kyau a gare shi ya yi martani kan zargin saboda duk wani mai riƙe da kujerar siyasa mai halaccin zama ɗan wata ƙasar, ka iya rasa kujerar sa kamar yadda dokokin tarayyar Najeriya suka yi tanadi.”

“Tinubu yana buƙatar ya hanzarta da gaggawa ya fito ya fayyace gaskiya kan wannan zargin, wanda yake zama babbar barazana ga kujerar shugabancin ƙasan da INEC tace ya lashe.”

Source: Hausa.legit.ng

Views: 4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *