Ana zargin wasu ƴaƴan jam’iyyar APC reshen Malumfashi da yin zagon ƙasa ga jam’iyyar

Wadanda Suka Shiga Jam’iyyar APC da Wata Manufa Sunfara Nuna Halinsu a Garin Malumfashi.

Dukda cewa Jam’iyyar APC jam’iyya ce wadda akasani da suna jam’iyyar MAJA wato Had’aka ahausance.

Wad’ansu da’ake zargin bata gari ne acikin jam’iyyar APC dake a k’aramar hukumar Malumfashi sunfara nuna rashin amincewarsu ga hukuncin da jam’iyyar ta yanke akan korafe-korafen da suka gabatar akwanakin da suka gabata.

Aranar 9 ga watan fabwari data gabata ne Jam’iyyar APC dake jihar Katsina tayi za’ben fitarda gwani na K’ananan hukumomin dake jihar, Kuma ansamu ‘yantakarkaru guda 4 a k’aramar hukumar Malumfashi wadanda suka had’a da Aminu Lawal Custom, Usman Umar Yaba, Maharazu Adamu Dayi Dakuma Abubakar Dabo.

Maharazu Adamu Dayi shine wanda Allah yabawa Nasarar chinye za’ben da Kuri’u 201, Sai Abubakar Dabo mai bimashi da Kuri’u 77 Aminu Lawal Custom wanda yazo na ukku da Kuri’u 70, Usman Umar Yaba Kuma yasamu Kuri’u 4.

Kwanaki kad’an Bayan Kaddamar da Maharazu Adamu Dayi Amatsayin Dantakara ajam’iyyar APC sai Abokanan takararshi suka fara suka da korafe-korafen tareda kai k’ara ga Uwar Jam’iyya cewa Maharazu Adamu Dayi Bai Chanchanta ba saboda dalilansu kamar haka:-

1- Maharazu Adamu Dayi yana aikin Gwamnati kuma bai ajiye aiki ba.

2- Maharazu Adamu Dayi yana aiki Amatsayin Mataimaki na Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Malumfashi da Kafur kuma yana karbar albashi guda biyu.

3- Maharazu Adamu Dayi Bashida Katin Jam’iyyar APC

4- Maharazu Adamu Dayi Bashida Sakamakon Allurar Korona.

Jim kad’an bayan mik’a korafe-korafen su ga jam’iyyar APC, jam’iyyar ta nemi Maharazu Adamu Dayi inda tabukaci yakare kanshi akan wadannan korafe-korafen, kuma yayi kamar yadda yakamata ta hanyar gabatar da hujjojinsa agaban teburin jam’iyyar.

Jam’iyyar APC ta gamsu da takardun da yagabatar kuma ta wanke shi kamar yanda dokar jam’iyyar ta tanada.

Sai gashi yanzu kuma wadannan Ƴan takarkaru suna nuna amincewa da hukuncin jam’iyya tahanyar Ɗaukaka kara da amfani da kafafen sadarwa wajen kawo rud’ani ga jam’iyyar APC.

Wad’ansu kuma Acikinsu suna ikirarin cewa zasu marawa jam’iyyar adawa ta PDP baya domin akayar da jam’iyyar APC azabe mai zuwa na k’ananan hukumomin, tahanyar zuwa majalisu daban-daban suna makarkashiya ga jam’iyyar APC da yunkurin tayarda tarzoma ga magoya baya.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *