Dalilin da yasa ake zargin Osinbajo da kawo rikicin addini a Najeriya

ZUWA GA FAROUK KPERROGI AKAN MAGANAR OSINBAJO!!

Daga farko dai ina yi wa babban marubuci kuma Malami Farfasa Farouk Kperogi gaisuwa irin ta addinin musulunci “Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta’ala Wabarakatuhu”.

Bayan haka: Tun jiya nake cin karo da mabanbantan ra’ayoyi akan wani dogon nazari da bincike da ka gudanar akan mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemin Osinbajo, wanda yake wannan bincike ya janyo cece-kuce, ya jefa shakka da tunani a zukatan su wasu ‘yan Najeriya musamman musulmai na Arewa da Kudanci. Wasu daga cikin ‘yan Najeriya musamman musulmai ‘yan Arewa sun amince da wannan bincike da ka gudanar akan mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemin Osinbajo.

Hakika zan iya cewa na ji dadin wannan bincike wanda ya tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemin Osinbajo mutun ne mai riko da addinin sa da kuma ganin addinin sa ya ci gaba. Mutun ne mai ilimin addinin sa, mutun ne mai kokari akan addinin sa tun kafin ya tsunduma a cikin siyasa har Allah ya kaddari ya zama mataimakin shugaban kasar nan.

To daga farko dai zan so na fara yi wa Farouk Kperogi wasu tambayoyi kafin na tsunduma a cikin rubutun da nake son gabatarwa;

Ka cire son zuciya, ka cire bangaranci, ka cire rashin adalci, ka ji tsoron Allah ka fadi gaskiya;

Shin tsakanin da Allah da Buhari ne yake riko da addinin musulunci irin yadda ka siffan Osinbajo za ka fito ka ce kada al’umma musammab ‘yan Arewa su zabe shi domin idan ya ci zabe zai musuluntar da Najeriya ko kawo rikici a cikin ta?

Shin tsakanin da Allah da Pantami ne yake riko da addinin musulunci irin yadda ka siffan Osinbajo za ka fito ka ce kada al’umma musamman ‘yan Arewa su zabe shi domin idan ya ci zabe zai musuluntar da Najeriya ko kawo rikici a cikin ta?

Shin tsakanin da Allah da dan Arewa ne yake riko da addinin musulunci irin yadda ka siffan Osinbajo za ka fito kace kada al’umma musamman ‘yan Arewa su zabe shi domin idan ya ci zabe zai musuluntar da Najeriya ko kawo rikici a cikin ta?

Na sani cewa ko hauka ta kama ka baza ka fadi hakan ba, domin na tabbata sai ka hadu da fushin ‘yan Arewa da musulmai, wanda hakan zai janyo maka bakin jinin da har ka koma ga Allah ‘yan Arewa baza su sake ganin mutuncin ka ba.

To abin tambaya a nan shine; Shin duk wanda ya yi riko da addinin sa mutumen banza ne?

Shin anya jahili yana riko da addinin sa kowa?

Tabbas duk wanda ya yi riko da addinin sa Musulmi ko Kirista zai kasance mutun mai adalci ga kowa, Kirista da Musulmi, marar addini harma ga dabbobi, domin daga cikin addinin Musulunci ko Kiristanci babu inda aka halatta zalunci.

Yau kowa ya san cewa Sheikh Isah Ali Pantami Malamin addinin musulunci ne, kuma mutun mai riko da addinin sa, kasancewar sa Malami kuma masanin addini hakan yasa Sheikh Pantami yake tafiyar da lamurran sa na Ministan Sadarwa kafada-da-kafada da Kiristoci dudda yake babu irin yarfen da ba su masa ba, babu irin cin zarafin da ba su masa ba. Wanda yake na tabbata da shi jahilin addinin sa ne da tuni ya yi rashin adalci a gare su, ta hanyar hana su damammakin da su ka samu a karkashin sa, wanda yake a addinance hakan ba daidai bane kasancewar Najeriya dunkulalliya kasa.

Baya ga haka: Yau halin da Arewa ta samu ta kanta miye banbancin sa da wanda kake magana?

Yau an wayi gari an mayar da musulman Arewa mabarata, an hana su zama gidajen su, an hana su gudanar da kasuwancin su, an hana u noma a gonakkin su, tattalin arzkin Arewa ya lalace, duk a lokacin da dan Arewa kuma musulmi yake jagorantar kasa.

Don haka siyasar 2023 bai kamata a zo mana da wani zancen banbancin addini ko bangaranci ba, Allah shi ne kadai ya san nagari a cikin musulmai ko Kiristoci, don haka a maimakon mu baiwa kan mu zabi zai fi kyau mu ba shi. Domin na shi zabi zai kasance alkairi koda kuwa daga farko mun kalle shi a zaman sharri. Kamar yadda zabin mu zai zama bahagon zabi koda kuwa daga farko mun kalle shi a zaman kyakykyawan zabi.

Daga karshe abin da kawai na sani shine; duk wanda ya san addinin musulunci ko Kiristanci dukkanin su babu addinin da yake goyon bayan fitina ko tashin hankali, kuma duk wando ya yi hakan to bai san addinin sa ba.

Najeriya dai kasar kowa ce, Kiristoci da musulmai, don haka doli ne kowa ya yi hakuri da wani.

Don haka mu dai muna rokon Allah madaukakin sarki da ya mana zabi nagari mafi alkairi.

S-bin Abdallah Sokoto

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *