Jam’iyyar APC, reshen jihar Legas ta bayyana a matsayin karya, rahoton da ke cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Bola Tinubu, ya yi watsi da takardun Naira a bainar jama’a a yayin babban taron jam’iyyar na karshe a Legas.
An yi gagarumin taron ne a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere a Legas.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Legas, Seye Oladejo, ya bayyana a wata sanarwa cewa, rahoton ya fito ne daga ‘yan adawar jam’iyyar da su ka yi mamakin nasarar taron.
Oladejo ya ce ƴan adawar siyasa sun koma yaɗa labarin watsi da Naira ga takararmu, Asiwaju Bola Tinubu.
Ya kara da cewa: “A wani rubutu da ke yawo a halin yanzu, rahoton da aka tsara ya nuna cewa Asiwaju Tinubu ya jefa wa taron jama’a da ke gefen hanya a Oshodi a lokacin da ayarinsa suka wuce daga filin jirgin saman Legas zuwa filin wasa na Teslim Balogun, Surulere, Legas.
“Ba komai ba ne face kazamar karya .https://apahausa.com.ng/ku-kalli-bidiyon-matar-da-ta-rusa-tarihin-kanawa/
“A ina Asiwaju ma ya ga tsabar kuɗi da har zai yi watsitsi da su?”
Kakakin ya ce da jam’iyyar ta yanke shawarar yin watsi da rahoton amma ta zabi fitar da sanarwar ne saboda wadanda za su iya yarda da rahoton.
source daily nigerian hausa
Views: 5
