Baƙuwa ta sace jariri awa ukku da haihuwar sa a jihar Nasarawa

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa.

Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata.

Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa.

Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata.

Badakalar Kudi: EFCC Ta Kwace Fasfo Din Betta Edu Da Sadiya Farouk Domin Hana Su Guduwa.

Aminiya ta ruwaito cewa bayan haihuwarsa da misalin karfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka mika jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su.

Wani ganau da ya nemi a boye sunasa ya ce, bayan sun dawo dakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata bakuwa, wadda ake zargin sun hada baki wajen sace jaririn.

‘Kamar Layar Zana’

A cewarsa, “’yar uwar mai jegon ce ta ce mata za ta koma gida ta dauko cajar wayarta da ta manta; shi ne ta hada ta da wata mata da za ta zauna da su kafin ta dawo ,” wadda ake zargin ita ce ta sace jaririn.

Sace jaririn daga dakin masu jegon da misalin karfe 6 na safe, awa uku da haihuwarsa ya jefa daukacin jami’ai da sauran mutanen asibitin cikin al’ajabi.

Wata ’yar uwar mai jegon da ta nemi a boye sunanta, ta tabbatar cewa, ’yar uwarsu ce kawo wa mai jegon wata bakuwa, ta kuma damka mata jaririn.

A cewarta, ba su yi aune ba, sai dai aka nemi jaririn da bakuwar — wadda ya yi zargin matsafiya ce — suka rasa, sun yi layar zana.

Ta ce, “Ba mu ga barauniyar jaririn ba, wannan wane irin rashin imani ne, mace ta shiga asibiti ta yaudari duk ’yan dakin da masu tsaron kofa cewa za ta yi masa wanka, amma ta tsere da jariri. Duniya ta zama abin tsoro!”

Yadda Aka Sace Jaririna —Mai Jego

Mai jegon, Malama Wasira Suleiman, wadda ke zubar da hawaye, ta ce “wadda aka kawo domin ta taimaka wajen kula da jaririn, ita ce ta sace jaririn da na dauka a cikina wata tara.

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *