Ba zamu fara aiki ba sai an biyamu alawus—INEC

Wasu ma’aikatan wucin-gadi na hukumar zaɓe a Najeriya sun ce ba za su fara aikin tantance masu kaɗa ƙuri’a ba har sai an biya su wasu alawus-alawus ɗinsu.

Ma’aikatan na Mazaɓar Ɗorayi Karama a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar, sun ce suna neman alawus ne na horaswar da INEC ɗin ta ba su.

Wakilin BBC Hausa a Kano Zahradden Lawan ya ce yanzu haka masu zaɓe na can sun yi cirko-cirko suna jiran ikon Allah.

Jihar Kano na da masu kaɗa ƙuri’a fiye da miliyan biyar, abin da ya sa jihar ta zama ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan takara suka fi kewayawa domin neman ƙuri’u.

source: bbchausa

Views: 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *