
Jaridar Labarai24 ta ruwaito labarin cewa, tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanatan shiyyar Kano ta tsakiya a zauren majalissar dattawan Najeriya, malam Ibrahim Shekarau ya ce shi fa siyasa a matsayin addini ya dauke ta, ga kadan daga cikin abinda rahoton ya kunsa.
Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ba zai taba daina siyasa ba face mutuwa ce ta cimmasa domin kuwa ya dauke ta a matsayin addini.
Tsohon Gwamnan Jihar ta Kano, ya yi wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai bayan kaddamar da Majalisar Shura a gidansa da ke Unguwar Mundubawa a birnin Kanon Dabo.
Malam Shekarau wanda ya yi gwamnan Kano tsawon wa’adi biyu kuma ya zama Ministan Ilimi a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya ce “bani da lokacin da zanyi ritaya daga siyasa har sai na mutu.
Shekarau wanda ke wakiltar Kano ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, ya ce, “dalilin da ya sa nake maimaita wannan batu shi ne, babu wani lokaci da zanyi ritaya daga siyasa, a cewarsa.
Menene ra’ayoyinku?
Views: 15
