Yadda zaka gane cewa ka mutu bayan an binne ka

Hausawa sun ce mutuwa rigar kowa, muna tafe da wani batu mai ratsa zuciya, ta yadda mutum zai gane cewa ya mutu.

Da farko idan Aka zare ran mutum zai ga kamar mafaki kake yi har masu wankan gawa su zo su cire maka kayan jikinka, su yi maka wanka a dauko ka a fito da kai a zo wajen sallar gawa bayan an gama a dauke ka zuwa makabarta.

Idan an je an saka ka cikin kabarin ka sai kaji ana cewa, “ga wani waje can bai samu kasa ba a kawo kasa a kara tura maka har kaji babban ami ninka yana cewa, ga wata kofa can a toshe ta kai ka rika kara kana kuka kana cewa.

Wai yaushe zan farka daga wannan mummunan mafarkin da nake, bayan an kammala rufe ka anyi addu’a kowa ya watse sai kani shuru sai kai kadai a cikin kabarin ka, sai Allah madaukakin sarki ya umarci mala’ikan daukar rai da ya maido maka da ran ka.

Bayan an dawo maka da shi sai ka farka ka bude idanunka sai kayi godiya ga Allah ka ce Allah na gode maka da ka sa na farka daga wannan mummunan mafarki da nake yi, sai ka yunkura za ka ta shi sai kayi an daure ka da rika wacce babu hannu babu wando.

Babu aljihu sai kai kadai a cikin rigar sai ka ga duhu kuma ka ga an matse kw cikin rami daga nan sai ka fahimci cewa cikin fa kasa kake ba a daki ba, tun daga nan sai ka gane cewa ashe fa da gaske ka mutu kuma a halin yanzu cikin kabarinka kake.

Idan kai dan aljanna ne za kaga mala’iku cikin kyakkyawar sura, idan kai dan wuta ne za su zo maka da mummunar kama Allah ya kyauta yasa mu cika da imani ameen.

Da fatan za kuyi shared zuwa sauran groups don yan uwa su amfana.

Views: 257

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *