Babban lauya ya shigar da kara kan a cire Najeriya daga cikin kasashen musulmin duniya

Shugaba Muhammadu Buhari

A watan daya gabata ne wani lauya mai suna Malcom Omirhobo a Najeriya ya shigar da kara domin neman cire kasar daga cikin jerin kasashen musulmin duniya.

Lauyan mai raajin kare yancin dan Adam ya shigar da Gwamnatin tarayya kara yana neman kotu ta haramta wa Nigeria cigaba da kasancewa mamba a kungiya kasashe musulmai ta duniya wato OIC (Organisation of Islamic Countries).

Lauyan mai suna, Malcom Omirhobo ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja ta kuma haramta wa duka jihohi 36 na Nigeria da Abuja daga alakanta kansu da wani addini ko nuna fifiko kan wani addini ko bin tsarin wani addini a hukumance a jihohinsu musamman na yankin kudu.

Lauyan ya kara da cewa Nigeria kasa ce ta kowa da kowa wacce ke dauke da mutane fiye da miliyan 200 dake bin addinai da al’adu daban-daban don haka zamewar Nigeria a matsayin mamba a kungiyar kasashen musulmi ya saba dokar kasa sannan tamkar nuna wa duniya ne cewa Nigeria kasar musulmi ce.

A cewarsa lauyan ya nemi kotu ta haramta wa Nigeria cigaba da kasancewa a OIC, ko bayar da wani tallafi ko gudunmuwa daga baitul malin kasar zuwa kungiyar ta OIC.

Kunji fa menene raayinku?

Views: 23

One thought on “Babban lauya ya shigar da kara kan a cire Najeriya daga cikin kasashen musulmin duniya

  1. Ai basai ya sa karaba daman aikin yahudawa take yi dune suka sashi yabyi wannan furucin Dan su kuma yahudawan su Mara mass bays su biya bukatansu in ba hakaba a cikin Nageriya musulmai sukafi yawa ko kuma kiristawa a yi hasashe again suwa sukafi yawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *