Bana Bukatar Namiji Kuma Ba Zatan Taba Yin Aure Ba – Inji Wata Mata Miloniya
Shahararren dan wasan barkwanci kuma dan wasan kwaikwayo, MC Mbakara kwanan nan ya tattauna da wata mata mai kudi wacce ba shakka tana da wani tunani ko ra’ayi na daban game da rayuwa.
MC Mbakara ya tunkari matar ne yayin da ya yaba mata kan katafaren ginin da ta gina wanda ta ce tuni ya kashe mata N86m.
Da take magana, matar wacce ba ta da aure, lokacin da aka tambaye ta dalilin, ta bayyana cewa ba ta bukatar namiji a rayuwarta.
A cewarta, ba za ta taba yin aure ba. MC Mbakara wanda ya bayyana cikin kaduwa da furucin ya tambaye ta dalilin hakan amma ta ce ita wannance sha’awarta ta.
MC Mbakara ya ci gaba da tambayarta ko zata iya saduwa, sai tace eh, ta ce za ta iya samun duk namijin da take so.
Wannan magana babu shakka ta bar MC Mbakara cikin kaduwa.
Meye Zakuce?
Daga Baba Waziri Net
Views: 16
