Bayan na sauka daga mulki zan rika zuwa gona ta ina duba shanu na a kullum—Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayya abinda zai mayar da hankali a kansa bayan ya sauka daga mulkin a kasar a shekarar 2023 mai zuwa, in da ya ce “Ina da gona ta da shanu na zan rika zuwa ina duba su a kullum bayan na sauka daga mulkin Najeriya a zaben 2023” in ji shi.

A wani labarin kuma shugaban ya ce

Ina fatan ƴan Najeriya za su yi min adalci idan za su ba da tarihina – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana fatan ƴan Najeriya za su yi masa adalci idan za su tuna da shi bayan ya sauka a kan karagar mulkin kasar nan.

Buhari ya faɗi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wakilin gidan talbijin din Arise ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Ya ce fatan sa shine a faɗi gaskiya, sannan a yi masa adalci idan za a bada labarin abubuwan da ya yi na ci gaba a kasar nan bayan ya sauka.

Views: 18

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *