Dan Najeriya yayi Wuff da ‘yar Indiya, Yace Babban Burinsa ya Cika a Rayuwa
Wani biki mai kayatarwa na wani ‘dan Najeriya da masoyiyarsa ‘yar Indiya ya kayatar da masu amfani da yanar gizo.
Kamar a shirin fina-finan kasashen ketare, masoyan sun shiga daga ciki a wani taro da suka yi mai kayatarwa a al’adar turawa.
Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun yi mamakin yadda masoyan basu duba bambancin da ke tsakaninsu ba, suka yi murnar aurensu.
Bidiyon bikin auren wani mutumi ‘dan Najeriya da masoyiyarsa ‘yar Indiya ya yi tashe a soshiyal midiya na dandalin TikTok.
‘Dan Najeriya yayi Wuff da ‘yar Indiya, Yace Babban Burinsa ya Cika a Rayuwa.
Faifan bidiyon da @grakeshotz a kafar ya wallafa ya tattara sama da jinjina 600 yayin da masoyan suka matukar kayatar da masu amfani da yanar gizo.
Sanye ka suturun Indiyawa, aka daura auren masoyan kamar a shirin fina-finan kasashen ketare.
Amaryar ta sanya sarkar kai kirar zinare, wacce ta zubo zuwa fuskarta da tafin hannayenta.
‘Yan soshiyal midiya sun bayyana ra’ayoyinsu game da bikin auren.
Ku latsa wannan Blue ɗin rubutun domin kallon Bidiyon 👇👇👇👇👇
@grakeshotz
Source: Hausa legit.ng
Views: 16
