
Mai girma ministan sadarwar Najeriya Dr. Sheikh Muhammad Ali Isa Pantami, ya bayyana irin adalcin da gwamnatin mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ke yi a kasar nan.
Inda ya ce gwamnatin shugaba Buhari na iya bakin kokarinta don magance matsalolin tsaro da cin hanci da rashawar da suka addabi kasar tsawon shekara da shekaru kawai dai wasu bata gari ne suke yi kafar ungulu da kan zabo a yunkurun gwamnatin na kawo cigaba a kasar nan.
Dr. Isa Ali Muhammad Pantami ya bayyana cewa a tarihin Najeriya ba’a taba samun gwamnati ko kuma ba’a taba kafa gwamnatin da take son ayi adalci ga kowa a kasar nan ba kamar wannan gwamnatin ta mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Views: 13
