
Wani fai fan bidiyo wanda ya rika yawo a kafafen sada zumunta na zamani wato social media ya nuna wani gungun mutane sun zagaye gawarwakin wadanda aka kashe lullube da ganye yayin da aka nuno wani malamin addinin kirista yana yin jawabi yana cewa
Musulmai sun zo sun kar kashe musu mabiyansu a har cikin unguwanninsu ba tare da sun yi musu laifin komai ba, wata mata mai suna Aisha ce ta wallafa wannan photon bidiyon a shafinta na Facebook wanda kuma bisa ga dukkan alamu an nadi fai fan bidiyon ne kai tsaye a dai dai lokacin da yake jawabin.
Duk da cewa sashin Hausa na APA bai tabbatar da sahihancin gaskiyar abinda ya faru da mamatan ba amma dai ita wacce ta dora photon bidiyon ta bayyana cewa al’ummar musulmai sun fara daukar fansa.
Nuna fatan Allah ya tsayar da wannan al’amari iya nan kuma ya kawo mana dauwamammen zaman lafiya ameen
Views: 8
