Mace ce ta lashe gasar karatun Alkur’ani mai girma a Jihar Zamfara.
Daga Junaidu Ahmadu Doro.
Budurwar da ta zo na Daya a gasar Musabakar karatun Al’kur’ani a jihar Zamfara ta sha Goma ta arziki.
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya Gwangwaje Yarinyar da ta lashe gasar musabakar Al’kur’ani da aka gudanar a jihar Zamfara da abin alkairi.
Ga dai Abubuwan da aka Bata kyauta :
-Na daya an Bata makuden Nairori.
-Na biyu an Bata gida Ginanne a birnin Potiskum na jihar Yobe.
-Na Uku an Bata Aikin yi.
-Na hudu an Bata kujerar aikin Umra ita da mijin da za ta Aura.
-Na biyar an Bata Dama ita da mijin da za ta aura su za6i Jami’ar da su ke so su tafi karatu a duk inda ta ke a fadin Duniya za a biya masu kyauta har su gama karatunsu.
Views: 12
