
Ƙasar Tunusia ta ci Najeriya 1-0 wanda hakan ya jawo aka fitar da ƙasar daga wasan na AFCON—2022.
Hakan na zuwa ne duk da irin ƙwarin gwiwar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bawa ƴan wasan inda ta gana d a su ta faifan bidiyo.
To ko me ya jawo wa ƙasar faɗuwa a wannan wasa?
Ga abinda wani ɗan Najeriya ke cewa.
Duk kasar data Ginu akan tsari irin na Kabilanci ko nuna Wariya ga Jinsin yare takan Gurgunta tsarin Cigabanta.
AHMAD MUSA DA UMAR SADIQ hazikan ‘yan wasa ne dake da fasaha da dabarun iya ratsa difendu don zira kwallo. Amma abin mamaki da takaici ace wai Ahmad musa sai Saura minti 2 atashi wasa aka sanya shi sabida rashin sanin daidai ko son zuciya.

HATTA ITA KANTA HUKUMAR NFF TANA BUKATAR GARAN BAWUL. DOMIN TSOHON MINISTA SOLOMON DALONG YA KARA DAGULA LAMURA A HUKUMAR LOKACIN DA YAKE MINISTA. adon haka garanbawul Tare da nada sabbin shugabanni masu kishi don shiga lungu da sakon Nigeria su zakulo hazikan matasa dake mutuwa a filin yakin kwallon kafa.
Views: 20
