Daga yau na fita daga addinin Kirista zuwa Musulunci kuma na canza suna daga Mercy zuwa Meenat

Jarumar da ta lashe lambar yabo ta Najeriya, Mercy Aigbe on ta bayyana sunanta na Musulunci a wata lacca da addu’o’i na musamman da ita da mijinta, Kazeem Adeoti suka shirya.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ta yi hira da ita inda ta ke zagayawa a shafukan sada zumunta, inda ta gabatar da kanta a sabuwar addininta.

“Sabon sunana Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah tare da H,” in ji jarumar.

Tattaunawar da aka yi a wurin laccar Ramadan da tauraro suka halarta a ranar Asabar, ta haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da intanet.

Views: 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *