Dalilan da suka sa matan China ba sa son haihuwa
“Ba na son ƴaƴa da yawa,’’ in ji Gloria, wata matar aure da ke da shekara 30.
Ta ce ta yi lissafin cewa hakan zai saka ta kashe kuɗi sama da $2,400 a wata bayaga sauran abubuwa da za ta buƙata na sayawa jariri a China.
“Zai kai kusan $436 a kowace rana kamar sayan abinci. $291 na kai yaro makaranta, $145 na kula da jariri, sai kuma akalla $1, 456 na sauran buƙatun makaranta.”
Gloria na aiki ne a matsayin malamar wucin gadi a wata makaranta da ke lardin Guangdong a kudancin China.
Kasancewa ita kaɗai ce a iyalinsu, saboda tsarin ƙasar China na ɗa tilo, ta ce tana son mayar da hankali kan biyan bashi da kuma adana kuɗi don taimaka wa iyayenta da suka fara tsufa.
Raguwar al’umma
China dai na fama da matsalar raguwar al’umma a karon farko cikin shekaru 60.
Sabbin alƙaluma sun nuna cewa yawancin mata a ƙasar na son su mallaki ɗa guda ɗaya ko kuma babu kwata-kwata.
Alƙaluman matan China da ba sa da yara ya tashi daga kashi 6 a 2015 zuwa kashi 10 a 2020, a cewar wani binciken da cibiyar kula da al’umma da kuma ci gaba na ƙasar ta gudanar a baya-bayan nan.
Binciken ya kuma nuna cewa matan ƙasar masu shekarun haihuwa ba sa da buƙatar samun ɗa, inda alƙaluman mata masu son yara ya ragu da kashi 1.64 a 2021, idan aka kwatanta da 1.76 a 2017.
Yayin da sauran ƙasashen Asiya kamar Singapore da Japan da Kudancin Korea, su ma suna da buƙatar haihuwar yara biyu kaɗai, yawancin matan sun ce yara biyu kaɗai suke so. Sai dai, ba haka batun yake ba a China.
“A China ba wai masu haihuwar ne suka yi ƙaranci ba, a’a, waɗanda ke buƙatar haihuwan ne ya ragu,’’ in ji Dakta Shuang Chen, mataimakin farfesa a fannin tsare-tsare na rayuwar ɗan adam a kwalejin harkokin tattalin arziki da kimiyyar siyasa da ke birnin Landan.
A dai-dai lokacin da China ke shirin gudanar da wasu tarukan siyasa – waɗanda ke da muhimmanci ga ƙasar – masu bayar da shawara kan harkokin siyasa, sun gabatar da takardu daban-daban na son bunƙasa yawan masu haihuwa.
Shawarwarin da suka bayar sun háɗa da taimaka wa matan da basu da aure yin ƙwayaye da rage kuɗin makaranta da na takardu daga makarantar firamare har zuwa kwaleji.
Har ila yau, akwai kuma shawara da suka bayar na bai wa yaran da aka haifa ba tare da aure ba kulawa kamar kowa.
A China, yaran da aka haifa ba tare da iyayensu sun yi aure ba, suna fuskantar wahalhalu wajen samun rajistar da ta dace na samun ilimi da lafiya da kuma na kyakkyawar rayuwa. Yawancin lokuta kuɗin suna tsadar gaske.
Source: bbchausa
Views: 40
