
Tun bayan ɓarkewar matsalar tsaron Najeriya jama’a suka yi ta caccakar malam ƙasar musamman Sheikh Isa Ali Pantami, kan yayi shuru gane da matsalar, sai dai ana ganin dalilin da yasa ya yi shuru shine saboda yana cikin gwamnati mai ci.
Amma kuma wasu bayanai sun bayyana cewa malamin yayi shuru ne saboda yana bawa shugaban kasar shawara game da matsalar tsaron a asirce kuma shugaban na saurarar sa kunga ba don haka ba da anga yana magana game da matsalar.
A makonnan ne kuma aka yi gobara a kasuwar Cash and Carry dake birnin Abuja inda aka ga jama’a na wasoson kayan mutane a kasuwar wanda hakan yasa malamin yayi magana kuma har ya yi kuka game da lamarin.
Har wasu daga cikin ƴan ƙasar suka dunga yin rubuce rubuce game da lamarin ga kaɗan daga ciki.
Ku latsa wannan link don Kallon bidiyon.
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=4225005640937999&id=100002858136881
INNALILLAHI WA’INNA ILLAIHIR’RAJU’UN
Halin Mu Kadai ya isa Muyi Bankwana da Zaman Lafiya,
Minister Malam Dr Isah Ali Pantami yayi KUKA kan Halin da Muke ciki a Yau tare da Nazarin inda muka Dusa Gobe,
Wasu har sun Chanza abun zuwa cewa “Duk Kashe Kashen da akeyi baiyi Kuka Ba sai da akayi GOBARA”
Yan-Uwa Muyi NAZARI idan har Mutun na cikin yanayin GOBARA Mutane nayi mashi SATA !
Yaushe muke Tinanin TA’ADDANCI zai Kare a Cikin Mu ??
Su wadancan Barayi ne da suka samu damar Mallakar Makami,
Ya kake Tinanin wanda zaiyima SATA dai-dai lokacin da kayan Ka ke Cin Wuta idan ya Samu Bindiga ko ya sameka inda baka iya yi mashi komi ??
TABBASS Halin da muke ciki abin KUKA ne ga dukkan mai dogon Nazari da Tinanin,
ALLAH ya Kyauta ya kawo mana Mafita,
Amiin,👏
Views: 22
