
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi tsayin daka wajen tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar.
ZABEN 2023: Buhari Yace Duk Wanda Talakawa Suka Zaba Shi Zai Damkawa Mulkin Najeriya
Daga Comr Abba Sani Pantami
Shugaban kasa Muhammadu yayi alkawarin za a gudanar da zaben gaskiya da amana ba za su yadda da magudin zabe ba, ya jaddada cewa duk wanda talakawa suka zaba shi zai damkawa mulkin Najeriya.
Na tabbata matukar shugaban kasa Muhammadu ya kamanta adalcin yin a zaben 2023 tabbass zai wanke laifinsa ga ‘yan Najeriya masu ganin bai iya mulki ba, wanda tin a farko talakawan Najeriya sun nuna ma Buhari kauna ta yin adalci idan yahau Mulki.
Kuma masu karatu ku rubuta ku ajiye ina mai tabbatar muku da zaku tuna da wannan kalmar tawa.
Muna kyautata zato ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da hadin guiwar shugaban hukumar INEC na kasa za suyi iya kokarin su na tabbatar da an kamanta adalci a zabe mai zuwa.
Muna da hujjoji da dama da suke tabbatar mana da InSha’Allah shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai bawa masu tunanin yin magudi mamaki, idan lokaci yayi zamu bayyana wasu kadan daga cikin hujjojin.
Views: 14
