Video: Kabiru Gombe maƙaryaci ne ɗan maula duk abinda ya faɗa kan mahaifiyar Tunubu ƙarya yake—Anas Dala

A makon daya gabata ne shahararren babban malamin izalar nan Sheikh Malam Kabiru Haruna Gombe ya yi wasu kalamai da ke nuna goyon baya ga ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressive Congress APC.

Kalaman da basu yiwa ƴaƴan wasu jam’iyyun hamayya daɗi ba irin su Hon Anas Abba Dala, wanda ya fito ƙarara ya soki lamirin malamin wanda yace Kabir Gomben maƙaryaci ne kuma mai son abin duniya.

Sai dai wasu daga cikin ɗaliban malamin irin su Datti Assalafy sun fito sun yi tsokaci game da kalaman na Hon Anas Abba Dalan.

SIYASA KENAN

Wannan mutumi ya fadi maganganu masu tsauri akan babban Malamin Izala Sheikh Kabir Gombe

Ya kamata Sheikh Kabir Gombe ya dauki matakin doka a kansa domin ya tsare mutuncinsa sannan ya kawar da wasi-wasi a zukatan Ahlussunnah game da zargin da ake musu sun karbo kwangila daga gurin Tinubu

Allah Ya sauwake

Views: 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *