
Kayan masarufi na ci gaba da yin tashin gwauron zabi a sassan Najeriya daban daban duk kuwa da cewa yanzu lokacin kakar amfanin gona ne wanda ya kamata ace farashin yana raguwa.
Kamar yadda aka saba bisa al’ada duk idan irin wannan lokacin na kakar girbe amfanin gona yayi farashinsa yana faɗuwa ƙasa war was, amma a shekarar bana ba haka abin yake ba domin kuwa.
Bisa ga rahotanni da muke samu daga sassan ƙasar daban daban na cewa farashin amfanin gonar na ƙara tashi sama, inda rahotanni daga jihar Legas ke cewa farashin buhun farin wake ya kai kimanin ₦100,000.
Yaya farashin yake a yankunanku da fatan za kuyi mana comments na farashin kayan masarufi a yankunanku.
Views: 23
