Addu’ar Talaka Ce Ta Kama Atiku Abubakar
Kamar yadda a wancan lokaci da yake kan konkoɗar giyar Mulki, Atiku Abubakar yayi ikirarin cewar Allah baya karɓar addu’ar Talakawa, yayi wannan ikirari ne a daidai lokacin da Talakawa ke Alqunutu ga gwamnatin su wanda Obasanjo ke jagoranta.
Tun shekarar da Atiku yayi wannan kalami har zuwa yanzu bai sake haɗa hanya da Nasara ba a dukkanin zaɓukan shugaban ƙasa da ya shiga.
Kar na kaiku da nisa, ko a wancan lokacin sai da Allah ya nuna masa izza da tasirin addu’ar Takala, domin sai da saɓani ya shiga tsakaninsa da shugaba Obasanjo har takai ga Obasanjo yayi yunkurin ajiye shi ya ɗauko sabon mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen da za’ayi na tazarcen su, Haka dai Dattawa suka sanya baki cikin rigimar har aka sasanta tsakaninsu.
Garemu Talakawan Najeriya, zamu zaɓi wanda tsabar tsagoran rashin mutunci da darajamu yayi katutu a zuciyar sa, wanda har ta kai ga yana ikirarin cewar addu’ar mu ba zata karɓu?
Kar mu manta mutumin da yake ganin cewar Talaka bashi da wata ƙima agurin Allah, yanzu shine zai dawo kuma yana neman Talaka ya rufa masa Asiri?
Views: 6
