
A yammacin ranar juma’a ne wasu shafukan sada zumunta na facebook suka riƙa yaɗa jita jitar dake cewa sojojin Najeriya sun hallaka ƙasurgumin mai satar jama’ar nan wato Turji.
Inda suke cewa Jami’an tsaro sun bindige gawurtaccen dan bindigar nan Bello Turji.
Labarai da mu ke samu sun nuna cewa ana kyautata zaton jami’an tsaro na sojoji a yankin Isah dake jihar Sokoto sun samu nasarar bindige gawurtaccen dan bindigar nan Bello Turji a wani bata kashi da akayi a jiya Alhamis.
Sai dai har yanzu mu na jiran cikakken rahoto daga wakilin mu na wannan yanki.
Sai a dakace mu.
Sai dai a zahirin gaskiya babu wata sanarwa daga ɓangaren jami’an tsaron da take nuna cewa sun kashe ɗan ta’addan.
Views: 39
