Gwarzon maza: Matashi ya auri mata biyu a tare kuma sun samu juna biyu a lokaci ɗaya
Wani matashi mijin wasu matasa mata guda biyu ya bayyana cewa dukkanin su sun haihu a lokaci ɗaya
Matashin ya bayyana cewa matan nasa a lokaci ɗaya suka samu juna biyu suka haifi wanda ya sanyawa sunan Pendo da Favian.
Ya sanya wani bidiyo a TikTok domin murnar wannan baiwa da ya samu, amma mutane sun yi bayyana mabambantan ra’ayoyi
Wani matashi ya yaɗu a manhajar TikTok bayan ya sanya bidiyon kyawawan matan sa guda biyu.
A wani bidiyo da ya sanya a shafin sa na TikTok mai suna, @wamaiyu, matashin ya bayyana cewa matan sa lokaci ɗaya suka samu juna biyu.
TikTok/@wamaiyu Asali: TikTok
Bayan kuma samun baiwar ɗaukar juna biyun su a tare, matashin ya kuma bayyana cewa matan nasa lokaci ɗaya suka haihu.
A cikin bidiyon, an nuna matan nasa ɗauke da rusheshen junan biyun yayin da ake ɗaukar su hoto suna cikin farin ciki.
Sai dai matashin bai nuna hotunan jariran da aka haifa masa ba, amma ya gayawa masu bibiyar sa cewa ya raɗa musu suna Pendo da Favian.
Mutane sun yi sharhi sosai a kai
Mutane da dama sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi akan bidiyon. A yayin da wasu suka yaba musu saboda haɗin kan su, wasu kuwa cewa suka yo ba zasu iya rayuwa da kishiya ba.
Source: hausa.legit.ng
Views: 18
