Hanyoyi 12 da mace zata yi amfani dasu wajen buɗe zuciyar Mijin ta da sabuwar soyayya

SHAFI NA 4
LITTAFIN (HANYOYI GUDA 12 DA ZAKI BUDE ZUCIYAR MIJINKI DA SABUWAR SOYAYYARKI)

SIRRI:- wani abune da mutun yake barinsa acikinsa batarada ya furtashi ga kowaba, abin yakan iya kasancewa mai kyau ko mara kyau, kuma fadar abin zai iya zama alkhairi ko barna
Misali:-


-Sirrin aure, mu’amalar dake shiga tsakanin mace da namiji ALLAH yayi hani afallasa wannan sirrin haramun ne afutardashi
((Manzan Allah (ﷺ)yace: “yana daga sharrin mutum Agurin ubangiji Abin saukarwa ranar Alkiyama miji ya biya bukatarsa ga matarsa itama tabiya bukatarta sannan dayansu yadai daita sirrin dan uwansa, muslim ne ya rawaeto”))

-Wannan sirrin shine yafi kowane sirri nauyi da girma acikin aure amma ayanzu wasu dayawa sun mayarda hakan ba komaiba duba da yadda ake terere dashi alungu da sako na social media, kai dazaka karanta kaine zakaji kunya

-Angwaye da amare aji tsoran ALLAH kudaina zubarwa da junanku mutunci a idan abokai da kawaye dan ALLAH

-Sirrin dangin kowane bangare (namiji da mace) anan wajen babu wani dacewa da tsari amatsayinku na ma’aurata kuna fadawa junanku sirrikan danginku,
Misali:-
Sata, shaye², ya wace², da makamantansu.
-Koda ace mijinki yakasance mai mai sakar baki naki kune

-Ki kiyaye bakinki, dadin hira ko gulma irinta ma’aurata yasa kiringa fadawa mijinki sirrukan yan’uwanki, wannan duk bai daceba babu tsari aciki, rashin sirrine hakan idan wataran yakasance mai gorine idan kunsamu sabani kece zaki kwana ciki

-Kiki yaye fadawa mijinki sirrinki tsakaninki da mahaliccinki, bawa miji labarin wani nau’in san zuciya dakika tabayi da sauransu, ALLAH ma bayasan mutum yaringa fallasa tarin zunubansa

Wasu zasuyi tunanin aure ba wasa bane ya wuce haka, akwana tashi dole zaka fadawa mijinka sirrukanka wannan ba gsky bane amahanga ta hankali hakanma bai daceba
-Idan kowane bangare na ma’aurata bai fadawa daya cigan danginsaba to akwai rashin dacewar fadar akasin hakan
Misali:-
Wasu mata dayawa wulakancin dasuke fuskanta daga wajen mijinsu yanada alaka da kwancewa kansu sirri dasukai shiyasa hakan yayi tasiri mazajen nasu ke ganin basuda wani galiwo ko mafuta daga dangin macen, shiyasa suke wulakantasu batarada nadama ba

-Ki rike sirrinki, sirrinki da mijinki daban mijinki shine naki kuma yasan wace ke, babu ke babu fadawa mijinki sirrin wasu kodan tsira da mutunci.
ALLAH yasa muzamo masu rike sirrukanmu Ameen

Source

Views: 26

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *