Hanyoyin da za kubi don magance matsalar munshari a cikin bacci

Shin Ya Kuke ji Idan Kuna Bacci Da Mai Munsahari? Ga Hanyoyin Da Za’a bi Domin Magance wa:

Lokacin da kake Munsahari, to na kusa da kai zai rinƙa jin wata ƙara mai ƙarfi saboda numfashin yana toshewa.

Hakanan yayin barci, akwai wata tsoka da ake kira da”mukƙwallato” da ke cikin makogwaron ku wanda ke taimakawa wajen jawo iska zuwa maƙoshi. Munsahari na iya haifar da ciwon kai, haki ko shakewa da daddare da ciwon kirji.


Wani ƙwararren likitan maƙogwaro, Mayoclinic  ya raba abubuwan da ke haifar da Munsahari;

  1. Bakin ka da yanayin yanda ka kwanta barci.

Idan idan muƙwallato da ke rataye a cikin ɓangarorin bakin ka ya yi tsawo, to zai iya toshe kwararar iska kuma zai rinƙa karkarwa hakan na haifar da Munsahari.

  1. Rashin bacci mai kyau.

Lokacin da ba ka samu isasshen barci ba, to idan ka kwanta hakan zai iya haifar da Munsahari, saboda makogwaron ka zai samun ƙarin Iskar shakatawa.

  1. Yawan shan barasa.

Idan ka sha barasa da yawa, musamman kafin lokacin kwanciya barci, zai sa tsokar makogwaro ta saki jiki da yawa, wanda hakan zai haifar da toshewa, ita kuma toshewa na haifar da Munsahari.

  1. Matsalolin hanci.

Idan kana da wasu matsalolin hanci kamar mura zai iya haifar da cunkoson hanci kuma hakan zai iya haifar da Munsahari, saboda numfashinka baya fita yanda ya kamata.

Hanyoyin da Za’a bi Domin Magance Munsahari

  1. Ka rinƙa yin amfani da magungunan rage ƙiba, idan kana da ita.
  2. Ka rinƙa kwanciya ta gefen ka na dama.
  3. Ka guji shan taba kuma ka iyakance shan barasa.
  4. Ka rinƙa samun isashshen Barci.
  5. Ka rinƙa yin Amfani da matashi wajen kwanciya.

Views: 67

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *