Har yanzu Ba’a kammala zaɓen jihar Kano ba akwai ƙura —Cewar Rarara

Mawaƙin yace anci amanar mutanen Kano, saboda haka ba zasu kyale ba, zasu ƙarbo nasarar APC a kotu.

:A wani Labarin Kuma:

Fitaccen mawaƙin siyasar nan a Najeriya Dauda Kahutu Rarara ya saki sabon faifan Bidiyon gargaɗi ga magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano Eng Rabi’u Musa Kwankwaso inda ya ya ce.

“Uwa daban ce bahaushe ma ya ce idan ana dara fidda Uwa ake saboda haka ku dakata kar wanda ya ƙara kiran mahaifiya ta da sunan banza ko yaci mutuncin ta, domin zan iya jure komai amma banda taɓa mahaifiya ta idan ba haka ba zamu haɗu Kotu da mutum komai girmansa” in ji mawaƙin.

A safiyar yau ne dai kafafen sada zumunta suka cika da kalmar “Tsuleliya” wacce ƴan Kwankwasiyya ke nufin mahaifiyar mawaƙin da ita, biyo bayan waƙar da ya saki a daren jiya mai taken “Tangal Tangal yaran Tsula”

Kalli bidiyon Rarara Nan https://youtu.be/Av2_2wwXE5s

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *