Hatsarin mota ya hallaka mutumin da ya yi zanen ɓatanci ga MANZON ALLAH SAW

Motar wanda ya yi zanen batanci ga Addini ta yi arangama da roka, ya mutu

Lars Vilks, mutumin da ya yi zanen batanci ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kasar Sweden cikin shekarar 2007, ya mutu a wani mummunan hadarin mota a ranar Lahadi.

Tun bayan da ya yi batancin ga Ma‘aiki, ‘yan sanda ne ke biye da shi don kare lafiyarsa.

Hadarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da shi ta yi arangama da roka.

‘Yan sanda guda biyu masu kula da shi suma sun rasa rayukansu a hadarin, wanda ya faru a kudancin garin Markaryd.

Wannan mai zane ya mutu, yana da shekaru 75 a duniya.

A watan Yulin wannan shekara, Kurt Westergaard, Baturen kasar Denmark da shi ma ya yi zanen batanci ga Manzon Allah (S.A.W) ya mutu.

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *