Ku latsa nan don kallon Bidiyon
Daga ƙarshe dai jiya Juma’a an ɗaura auren matashin nan mai suna Isyaku mai Baro wanda yaƙi yarda ya karɓi kyautar kamfanin buga ruwan Pure-Water da tsabar kuɗi Naira Miliyan 20 da kuma motar hawa ta kimanin Naira Miliyan 4 da ginannen gida a GRA Kano don ya rabu da Budurwar sa kamar yadda abokin karawar sa ya yi masa tayi. Ku kalli wannan bidiyon
Alhaji Abubakar Mai Shadda wani hamshaƙin attajiri ne dake saffarar kaya daga Dubai zuwa Najeriya shine yaga yarinyar taje siyayya tare da ƙawayenta a ɗaya daga cikin kantunan sa a daren jiya inda yace yana sonta kuma ya nace yayin da shi kuma saurayin yarinyar sana’ar tura baro yake a kasuwar Kantin Kwari kwana 2 ya rage a ɗaura mata aure inda Allah Abubakar ya ce dole sai ya aure ta amma bai yi nasara ba yayin da a ɓangaren iyayen yarinyar mahaifanta yace babu abinda zai hana aurenta da Isyaku sai mutuwa ko kuma shi yace ya janye,.
Rahotanni sun ce ƴan’uwa da abokan arziƙi sun rarrashe shi a kan ya janye wa Alhaji Abubakar ya haƙura ya nemi wata saboda dukiyar da za a ba shi ko mata huɗu yake so zai iya aura, amma ya kafe kan cewa mutuwa ce kawai zata raba shi da ita saboda haka ko dukkan dukiyarsa zai ba shi ba zai karɓa ba yafi son Maryam ɗinsa, sai gashi an ɗaura auren a ranar Juma’a, a cikin wannan hoton Bidiyon da aka ɗora a shafin intanet ya nuna su cikin farin ciki inda abokansa ke masa dariya cewa bai da rabon arziki
Kunji fa masoyi na gaskiya ko zaka iya yin irin wannan soyayyar ta matashin nan?
Views: 43
