VIDEI: “Wata budurwar ta koma gidan su saurayinta da kwana inda tace dole sai ya aure ta”

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Matarsa t ce, ka je wajen ɗan uwanka

ɗan majalisa ko Allah zai sa ya ɗan taimaka maka da wani abu.

Yaje wajen ɗan uwansa, ya gaya masa irin halin da yake ciki na wahala da kuma buƙatar taimakonsa.

Ya ɗakko sabbin kaya ya ba shi, ya ce kasaka kazo office gobe da safe ka sameni.

Da zuwansa sai ɗan uwansa ya ce, ka yi shiru da bakinka, kar ka ce komai, duk maganar da za a yi.

Ya ɗau waya y kira ɗan kwangila ya ce, ka yi haƙuri, kwangilar d zan baka na fasa, don na samu wani sabon ɗan kwangilar da ya bada abin da yafi naka.

Ɗan kwangila ya ce, Ran kai daɗe a yi haƙuri, gani nan zuwa office ɗinka don mu daidaita. Ya ce, sai ka ƙaraso.

Da zuwansa ɗan majalisa ya ce, ga ɗan kwangilar nan a zaune, ya ƙara Miliyan 6 akan yadda muka rabu da kai. Tun da mun daɗe muna mu’amala da kai, kuma na yi maka alƙawari, ka ba shi miliyan 6 ya bar maka aikin gaba ɗaya…..!

Ɗan kwangila ya ce, babu komai ran kai daɗe, zan bayar. Take y saka yaronsa ya je y amso kuɗi daga banki ya ajiyesu a gaban wannan ɗan majalisa.

Ɗan uwan (Talakan) ya ce, ina zaune ƙiƙam kamar ɗaya daga cikin gunkin jahiliyya.

Bayan an kammala komai, ɗan kwangila ya karbi takardun kwangila ya tafi. Ɗan uwana Ya ƙirga 1m ya bani, ya ce ga wannan ka rage zafi.

Da shigarsa gida, matarsa ta ce, ya kuka ƙare? Ya ce, akan idona ɗan uwana ya sacen 5m…!

Rubutawa: Sukairaj Hafiz Imam

Views: 37

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *