A wani shirin talabijin da ake yaɗawa kai tsaye a dandalin DCL Hausa shahararriyar jarumar fina finan Hausa ta Kannywood Hadiza Aliyu Gabon ta ce tana damuwa game da irin maganganun da jama’a ke yi a kanta.
Hadiza tace idan kaje wani taro gidan biki ko suna sai kaji ana cewa taƙi yin aure kuma ba haka bane shi aure lokaci ne idan lokacin sa bai yi ba mutum bai isa yayi ba.
Shirin wanda wakiliyar sashin Hausa na DW Binta Aliyu Zurmi ke jagoranta ya tattauna da mashahuran mata da suka haɗa Hadiza Aliyu Gabon Mrs. Mahuta inda daga ƙarshe Hadiza Gabon tace za tayi aure.

Da zarar ta samu namiji mai tausayi da riƙon addini wanda zai riƙeta bisa gaskiya da riƙon amana, Gabon ta ƙara da cewa, wasu suna tsoron tunkararta da maganar aure saboda tana da dukiya zata iya musu wulaƙanci da sauransu kuma wannan ba shine ba.
A wani labarin kuma.
Ƴan Sandan Nijeriya Sun Cika Hannu Da Yaron Da Yayi Garkuwa Da Mahaifinsa.
‘Yan sanda a jihar Kwara sun kama wani yaro Mai suna Issa Naigheti, wanda ake zargi da hada baki da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da mahaifinsa.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar na yaki da masu garkuwa da mutane sun kama Naigheti ne a ranar 4 ga watan Janairu, 2023 a Kambi kan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi ya amsa laifin hada baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa.
“Mambobin rundunar ‘yan sanda da ke yaki da masu garkuwa da mutane sun kama wani Issa Naigheti “m” a ranar 4/1/2023 a kusa da unguwar Kambi da ke Ilorin yayin da ake bin sahun masu garkuwa da mutane; A yayin da ake tattaunawa da shi ya bayyana cewa ya hada baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa, daya Bature Naigboho “m,” a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo, kuma an karbo kudi #2.5 miliyan a matsayin kudin fansa.
Ana ci gaba da kokarin damke sauran wadanda ke da hannu a lamarin, kuma za a mika karar zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin.
“Kwamishanan ‘yan sandan ya nanata kudurin sa na samar da ingantaccen yanayi domin gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali,” in ji PPRO.
RAHOTO -Aliyu shu’aibu Aliyu (MARIRI?
Views: 378
