HOTUNA: “Har yanzu akwai shaidar tsagewar bangon Ka’aba tun ranar da aka haifi Sayyadi Ali

Har yanzu akwai Shedar Tsagewar Bangon Ka’aba tun Ranar da aka haifi Sayyadi Ali.

Shedar tsagewar na nan daidai ruknul-yamani , kan kwanar Ka’aba. Kuma duk da akan yi kokarin rufe tsagewar ginin, amma wannan tsagewar na kara bayyana duk shekara tun daga ranar da aka haifi Sayyadi Ali (as) a cikin Ka’aba.

Al’amarin ya faru ne ranar 13 ga watan Rajab, shekaru 23 kafin hijra, a yayin da Mahaifiyar Imam Ali (as) Sayyida Fatima Bnt Assad amincin Allah ya tabbata agareta ta gamu da ciwon nakuda sanda take dawafi a dakin Allah’Ka’aba, sai ta roki Allah T da ya sawwaka mata halin da take ciki na nakuda, Kamar yadda Yazid bn Qanab, Sahabin Manzon Allah;S) yace ;

“ Muna zaune tare da Abbas bn AbdulMutallib muna fuskantar dakin Allah, sai muka ga Fatima bnt Asad a halin naquda, tana addu’a tana mai fadin, Ya Allah nayi imani da Kai da dukkan Manzanninka da Littafanka saukakku, Nayi imani da abin da Annabi Ibraheem wanda ya gina wannan dakin (Baitil Atiq) ya zo dashi, Ka sawwaka min haihuwarnan albarkacin Ibraheem da ‘Dan da nake dauke da shi “

Sai muka ga bangon Ka’aba ya tsage nan take, sai Fatima bnt Assad ta shige cikin Ka’aba ta inda ya dare kuma sai ta bace muka dena ganinta, sannan bangon ya sake komawa ya hade.

Sai muka fahimci wannan al’amarin na Allah ne,

Bayan kwana hudu 4, sai Fatima bnt Asad ta fito daga cikin Ka’aban dauke da Imam Ali (as) .”

Malaman Ahlullsunnah sun tabbatar da haihuwar Imam Ali (AS) a cikin Dakin Ka’aba kamar haka, ga kadan daga cikinsu.

1, Mustadrak, Imam Hakim , j 4, s 197
2,Sharh-ush-Shifa, j 1, s 327.
3, Nurul-Absar, Shablanji, s 183
4, Izalatul Khulafa , j 4, s 299
5, Marujud Dhahab; Mas’udi, j 2, s 311.

K.M. Inuwa 13th Rajab, 1444AH.

Views: 31

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *