Shugaban ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ibraheem Ra’isi, ya kira kungiyoyin Mayakan Falasdinu a waya, sun kuma tattauna akan yadda zai taimaka musu.
Masallacin Al-Ameen Muhammad dake Khan Yunus Kudancin Gaza, Makami mai linzami daga Isra’ila ya dagar-gazashi.
Kuma dai Isra’ilan ta kuma kaiwa Beit Hanoun dake Arewacin ƙasar ta Falasdinu hari yanzu haka.
Babban Jami’in Hizbullah, Hashem Safieddine yana cewa “Ba mu da tsaka-tsaki a wannan yaƙin” … harin da muka kai a Shebas, saƙo ne, muna gaya wa Isra’ilawa da Amurka su daina wannan “wauta” ko kuma dukan yankin (Na Isra’ila) za su shiga cikin yaƙin”, ma’ana zasu farmaki ƙasar ta Isra’ila ta kowane sashe.
Netanyahu ya sanar da cewa, Isra’ila ta fara killace Gaza, kuma za ta katse dukkan wutar lantarki, man fetur, da sauran kayayyakin da ke shigowa Gaza ta cikin Isra’ila.
Mataimakin Sakatare-Janar na kungiyar Islamic Jihad, Muhammad al-Hindi, ya shaidawa Al Jazeera cewa: “Isra’ila ta rude, kuma ba za ta iya killace Gaza ba.”
Muhd Bala Afuwa
Views: 16
