HOTUNA: Labarin yadda wani saurayi ya Auri Mata 7 a rana ɗaya

HOTUNA: Labarin yadda wani saurayi ya Mata 7 a rana ɗaya.

Wani mutum mai suna Habib Nsikonnene ya angwance da tsala-tsalan yan mata bakwai a rana daya
Habib wanda ya kasance shahararren dan kasuwa ya gwangwaje matan nasa da sabbin motoci a ranar bikinsu
Matashin angon ya kuma bayyana aniyarsa na kara wasu matan a nan gaba.

Wani babban dan kasuwa a kasar Uganda, Habib Nsikonnene, ya auri mata bakwai a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba a kasarsu.

Kamar yadda Capital FM Uganda ta rahoto, biyu daga cikin matan nasa sun kasance yan uwa na jini.

Nsikonnene ya auri Mariam, Madinah, Aisha, Zainabu, Fatuma, Rashida, da Musanyusa, wacce aka rahoto cewa ita ce uwargidarsa kuma sun shafe tsawon shekaru bakwai tare.

Ina da burin kara wasu matan a gaba – Ango Habib

Har ila yau, an rahoto cewa Nsikonnene ya siya sabbin motoci inda ya gabatarwa kowannensu a matsayin kyauta, kuma kowacce na dauke da sunanta a jikin motarta.

Da yake jawabi a wajen liyafar bikin, angon ya jinjinawa matan nasa kan zamowa masu biyayya a gare shi.

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *