HOTUNA: “Matsin rayuwa yasa wani mutum hawa kan rufin Masallaci ya cire kwanon a jihar Jigawa”

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

MATSIN RAYUWA: Wani Mutum Ya Cire Fara Rufin Kwanon Masallacin Da Ya Gina Shekaru 30 Da Suka Wuce

Al’amarin ya faru ne a Birnin Kudu dake jihar Jigawa, lamarin da ya razana al’umma.

Shi dai wannan bawan Allah wanda aka sakaya sunansa shine ainihin wanda ya gina Masallacin tsawon shekaru talatin da suka shuɗe, sai yanayin matsin rayuwa tasa ya ga ya dace ya gina shaguna a wani ragowar filin harabar Masallacin, lamarin da mutane sukace basu san wannan ba, tunda ya riga ya gina Masallacin ya barwa al’umma.

Dalilin haka ya fusata ya hau ya fara cire rufin kwanon Masallacin da zummar ya fasa yin Masallacin.

Views: 22

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *