Matashin da Ya Kashe Amaryar Babansa, Ya kuma Kashe Ƙanwarta, Yayi Bayani a wani bidiyo inda ya ce da sukun direba ya Huda mata a wuya sannan ya shake diyar yarta Mai shekaru takwas da zani a wuya.
An ce dai amaryar shekaru biyu kenan da aure kuma tana da ciki a yayin da ya kashe ta.

Yanzu haka dai matashin yana hannun jami’an tsaro inda yake amsa tuhuma a ɓangaren binciken miyagun laifuffuka.
A wani labarin kuma
Allah ya yiwa sarkin yakin Ringim Alhaji Shehu Uba Ladan rasuwa a jiya da dare bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya da yayi.
Kafun rasuwarshi ya rike shugaban Bankin Saving and Loan Bank na Ringim daga bisani ya zama shugaban Bankin na jihar Jigawa baki daya.
Sarkin yakin Ringim mutum ne mai matukar kirki da son al-umma da son zumunci da taimakawa al-umma.
Muna mishi Addu’ar Allah ya jikanshi ya gafarta mishi idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Views: 15
